10 Yuni 2021 - 10:31
​Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadin Yanke Albashin Ma’aikatan Kotuna Da Majalisun Jihohi

Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan ma’aikatan kotuna da na Majalisun Dokokin Jihohi su janye yajin aikin da suke yi, su koma bakin aikin su cikin gaggawa, idan kuma ba haka ba za a yanke albashinsu.

ABNA24 : Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar, inda yake yi masu gargadin cewa idan ba su koma aiki ba, to Gwamnatin Tarayya za ta tilasta yin amfani da dokar rike albashin wanda bai je aiki ba.

Ya ce ba ya fatan ganin lamarin har ya kai ga matakin da ma’aikatarsa za ta rike albashin ma’aikata, musamman ma ganin cewa an fara samun nasara a tattaunawar da aka fara su tun a cikin makon farko na watan Mayun da ya gabata.

To sai bayan fitar da wannan bayani na ministan kwadagon, kungiyar ma'aikatan shari'a ta sanar da janye yajin aikin da ma'aikatan shari'ar suke yi.

342/